Vous êtes sur la page 1sur 3

Wasikar Jagora Imam Khamenei Ga Matasan Kasashen Turai Da Arewacin

Amurka
21/01/2015
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Zuwa Ga Dukkanin Matasan Kasashen Turai Da Arewacin Amurka
Lamurrann baya-bayan nan da suka faru a kasar
Faransa da makamantansu a wasu kasashen
Yammaci, su ne suka sanya ni ganin ya dace in yi
magana da ku kai tsaye. Ina magana da ku ne, Ya
ku matasa; ba wai saboda na raina iyayenku ba,
face dai sai saboda ku ne manyan gobe, wadanda
makomar al'umma da kuma kasarku take
hannunsu; sannan kuma saboda ina ganin
zukatanku cike suke da neman sanin gaskiya.
Haka nan kuma ba wai ina magana ne da yan
siyasa da jami'an gwamnatocinku ba ne, don kuwa
na yi amanna da cewa da gangan sannan kuma da saninsu suka kawar da siyasarsu daga tafarkin
gaskiya da hakika.
Magana ta da ku kan Musulunci ne, musamman ma dangane irin abin da ake gabatar muku da shi
a matsayin Musuluncin.
Tsawon shekaru ashirin din da suka gabata zuwa sama - wato tun daga lokacin rugujewar
Tarayyar Sobiyeti - an gudanar da gagarumin kokarin bayyanar da wannan addini mai girma a
matsayin wani gagarumin abin tsoro. Abin bakin cikin shi ne cewa irin wannan yanayi na sanya
tsoro da kyamar (wannan addini) wani lamari ne mai tsoron tarihi cikin tarihin siyasar kasashen
yammaci.
Ni dai a nan ba ina so ne in yi magana dangane da irin kyama da tsoratarwa' daban-daban da ya
zuwa yanzu aka sanya cikin zukatan al'ummomin kasashen yammaci ba. Idan kuka koma kadan
cikin tarihi, za ku ga cewa sabbin marubuta tarihi, sun soki mu'amalar rashin adalci da gaskiya
da gwamnatocin yammaci suka yi wa al'ummomi da al'adun duniya. Tarihin Turai da Amurka ya
rusunar da kansa cikin kunya saboda bautar da mutane, mulkin mallaka da kuma zaluntar
wadanda ba fararen fata da kuma wadanda ba Kiristoci ba da suka yi. Masana da malaman
tarihinku suna cikin kunyar irin zubar da jinin da aka yi da sunan addini tsakanin mabiya darikar
Katolika da Protestant ko kuma da sunan yan kasanci da kabilanci a yakukuwan duniya na daya
da na biyu. Shi kansa hakan wani abin jinjinawa ne.
Manufar bijiro da wani bangare na wannan doguwar fehrisa na abubuwan da suka faru, ba ita ce
sukar tarihi ba, face dai abin da nake so shi ne ku tambayi masananku shin me ya sa a koda
yaushe sai bayan jinkiri na gomomin shekaru ko kuma ma daruruwan shekaru ne lamirin
al'ummomin yammaci ya ke farkawa da kuma dawowa cikin hayacinsa? Me ya sa ake damfara
lamirin mutane ga abubuwan da suka faru cikin tarihin shekaru aru aru ba batutuwan da suke
faruwa a halin yanzu ba? Me ya sa ake kange mutane daga fahimtar lamurra masu muhimmanci

irin su hanyoyin mu'amala da al'adu da kuma tunani na Musulunci?


Ku da kanku kun san cewa wulakanci da haifar da kiyayya da kirkirar tsoron sauran mutane na
boge, suna a matsayin wani fage ne da aka yi tarayya cikinsa wajen haifar da dukkanin irin
wadannan zalunci da mummunan amfani da mutane. A halin yanzu ina son tambayarku, shin me
ya sa yanzu aka dawo da tsohuwar siyasar sanya tsoro da kyamar Musulunci da musulmi? Me ya
sa tsarin mulki na duniya a halin yanzu ya sanya tunani na Musulunci a gaba? Shin wasu
abubuwa ne da suke cikin tunani da koyarwar Musulunci da har zai zamanto kafar ungulu ga
tsare-tsare da siyasar manyan kasashen duniya, sannan kuma me za su samu wajen bakanta
fuskar Musulunci?
A saboda haka, bukata ta ta farko ita ce ku yi tambaya da kuma binciko dalilin irin wannan
gagarumin kokari na bata sunan Musulunci.
Bukata ta ta biyu, ita ce yayin mayar da martani ga irin wannan gagarumin bakar farfagandar
bata sunan Musulunci (da ake yi), ku yi kokarin fahimtar wannan addini (Musulunci) da
koyarwar ta hakika kai tsaye. Lafiyayyen hankali yana hukumta wajibcin sanin hakikanin abin da
ake tsoratar da ku shi da kuma nesanta ku daga gare shi. Ni dai ba ina cewa ne lalle sai kun yarda
da fahimta ta ko fahimtar wani kan Musulunci ba, sai dai abin da nake cewa shi ne kada ku bari a
kange ku daga wannan hakikar wacce take da tasiri cikin duniyar yau saboda cimma wata bakar
manufa. Kada ku bari cikin riya su gabatar muku da yan ta'addan da suke karkashin ikonsu a
matsayin wakilan Musulunci. Kamata yayi ku fahimci Musulunci daga tushensa na asali. Ku
fahimci Musulunci ta hanyar Alkur'ani da rayuwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi da Alayensa).
A nan ina son in tambaye ku, shin ya zuwa yanzu kun taba karanta Alkur'anin musulmi kai
tsaye? Shin kun taba karantar koyarwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi da Alayensa) da kyawawan halaye da yan'adamtakarsa? Shin ya zuwa yanzu kun
fahimci sakon Musulunci ta wata kafa ta daban, ba kafar watsa labarai ba? Shin kun taba
tambayar kanku ya ya aka yi wannan Musuluncin, sannan bisa wasu koyarwa ya samu daman
zama mafi girman al'adu da ci gaban ilimi da tunani na duniya sannan kuma ya tarbiyyantar da
mafi girma da kyawun masana da masu tunani na duniya?
Ina kiranku da kada ku bari a yi amfani da bakar siyasa da wauta wajen katange ku daga gaskiya,
da kuma kawar da yiyuwar yin alkalanci cikin adalci daga gare ku. A halin yanzu da kafafen
sadarwa suka rusa ganuwar kan iyakokin kasashe, kada ku bari a kange ku cikin kirkirarrun kan
iyakoki na boge. Duk da cewa babu wani mutum, a kan kansa, da zai cike wannan gibin da aka
samar, amma kowane guda daga cikinku zai iya samar da gadar tunani da adalci a kan wannan
gibin da aka haifar. Duk da cewa wannan kalubalen da aka kirkira tsakanin Musulunci da ku
matasa wani kalubale ne mai sarkakiyar gaske, to amma hakan yana iya kirkiro sabbin
tambayoyi cikin zukatanku da suke neman sanin hakika. Kokari wajen samo amsoshin wadannan
tambayoyi, zai samar muku da wata dama ta gano wasu sabbin gaskiyar.
A saboda haka, kada ku bari wannan dama ta fahimtar gaskiyar Musulunci ta kubuce muku, don
me yiyuwa ta hanyar wannan jin nauyi a jika da kuke da shi, al'ummomi masu zuwa za su rubuta
tarihin irin wannan mu'amala da kasashen yammaci suka yi da Musulunci cikin sauki ba tare da

wahala ba.
Sayyid Ali Khamenei
1/11/1393
(21/01/2015)

Vous aimerez peut-être aussi